Asusun yara na majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta tarayya da su soke hukuncin da kotun Musuluncin jihar Kano ta yankewa wanda ya yi ɓatanci ga Allah S. W. A.
UNICEF ta ce babu adalci a ɗaurin shekara 10 da aiki mara wahala da kotun ta yanke wa Omar Farouq saboda munanan kalaman da ya furta ga Allah.
Wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins, ya ce, “Yanke wa yaron Omar Farouk mai shekara 13 – hukuncin ɗaurin shekara 10 a kurkuku da aiki mara wahala kuskure ne.
“Hukuncin ya saɓawa ginshiƙan kare haƙƙin yara da yi musu adalci a Najeriya da ma jihar Kano ta sanyawa hannu”.
Don haka ya yi kira da a “hanzarta amincewa da ƙudurin dokar kare yara ta jihar Kano domin tabbatar da cewa dukkannin yara ’yan ƙasa da shekara 18, har da Omar Farouq da sauran yara a Kano sun samu kulawa daidai da tsarin kare haƙƙin yara”.
A ranar 4 ga watan Maris ce Omar Farouq ya yi mummunan furuci ga Allah S.W.A a lokacin wata zazzafar muhawara.
Bayan saurayin a ƙashin kansa ya yi iƙirarin aikata laifin ne alƙalin kotun Shari’ar Musuluncin, Khadi Muhammad Ali-Kani ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 10 da aiki mara wahala.