Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kammala shirye-shiryen horar da ma’aikatan lafiya kan samar da ingantattun ayyuka don magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a jihar Adamawa.
Wakiliyar UNICEF a kasar Christian Munduate, ta shaida wa manema labarai jim kadan bayan ta duba cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na Yelwa a Yola, babban birnin jihar a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: NRC Ta Baiwa Fasinjojin Jingin Kasan Abuja-Kaduna Hakuri Kan Matsalar Karancin Man Dizal
Munduate, wanda bata bayyana adadin wadanda suka halarci taron ba, ta ce an shirya atisayen horon ta yanar gizo ne ga ma’aikatan hukumar kula da lafiya matakin farko ta Adamawa.
Ta ce an fara shirin ne a watan Disambar shekarar 2022, domin tabbatar da inganta karfin ma’aikatan lafiya.
“Lokacin da aka fara kirkire-kirkire, za mu ga yadda za ta bunkasa da kuma abin da za a kara tallafa mana mu yi shi ma.
“Saboda yana da matukar mahimmanci za mu iya samun hanyar nazari, hadaddiyar sabis yayin da muke magana game da abinci mai gina jiki.
“A gare mu, yaron ya zo na farko kuma daya daga cikin abu na farko da za a ba wa yaro shi ne damar da za ta rayu cikin koshin lafiya,” in ji ta.
Wakilin kasar ya lura cewa rashin abinci mai gina jiki barazana ce ga rayuwar yara.
Ta kuma bukaci kungiyoyin yada labarai a Najeriya suma su inganta abinci mai gina jiki da kuma shayar da jarirai nonon uwa zalla na tsawon watanni shida na farko.
Jami’ar ta UNICEF ta kara da cewa, babu abin da iyaye mata ke bukata illa shan ruwa da cin abinci mai kyau don samar da madarar da za su samu damar shayar da ‘ya’yansu yadda ya kamata.NAN.
A wani labarin kuma, Mambobin Jam’iyya Mai Kayan Dadi Sun Cire Jar Hula Sun Koma PDP
Tsohon sakataren NNPP na shiyya kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Sanata Rabiu Kwankwaso, Dr Babayo Liman da shugabannin kananan hukumomi 17 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a jihar yobe.
Sun bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da tsohon sakataren jam’iyyar NNPP na shiyyar da sauran wadanda suka sauya sheka suka yi wa manema labarai karin haske a sakatariyar NUJ da ke Damaturu.