Wani bincike ya tabbatar da cewa fiye da yara miliyan 10 ke fuskantar karamcin abinci a Afrika.
A wani matakin gaugawa da take shirin dauka akan alkalummanda aka bayyana , Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF , yace alkaluman zun zarce adadin da ake dashi da miliyan uku wata biyu da suka gabata.
UNICEF dai ta bayyana cewa, sai an samu kuɗaɗe da ruwan sama za a iya tunkarar matsalar maca macen yara a yankin Afrika.
Babbar jami’ar UNICEF Catherine ta fadawa BBC cewa wannan farin shine mafi muni da a ka fuskanta cikin shekaru 40.
Catherine tace ana mayarda hankali sosai a kan mastalar yaƙin ] yayinda ba amayar da hankali yadda ya kamata a yankin Afrika.
Ta bayyana cewa UNICEF na bukatar kuɗi da Yawan sun ya kai dallar Amurka miliyan 250, domin ayyukan agaji a ƙasashen Etofiya , somaliaya.
A wani labari Kuma na daban.
An gurfanar da wasu Mutum biyu a gaban Kotu, kan zargin satar na’urar sanyaya daki
An gurfanar da wasu mutane biyu Joseph Simon mai shekaru 25 da Oseni Meco mai shekaru 22 a ranar Talatar da ta gabata a gaban wata kotun Majistare da ke Ejigbo na jihar Legas.
Wadanda ake tuhumar, wadanda ba a bayyana adireshinsu ba, suna fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, sata da karbar kayayyakin sata.
Dan sanda mai shigar da kara, Insfecta Benedict Aigbokhan, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar da sauran su, sun aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Afrilu da misalin karfe 3:30 na rana, a makarantar koyar da addinin islama ta Soundhope dake Baruwa na yankin Ipaja a jihar Legas.
Ya ce wanda ake kara na farko, Simon, ya saci na’urar sanyaya daki guda hudu, wanda kudinsa ya kai Naira 300,000, mallakar Soundhope International Muslim Academy.
Aigbokhan ya kuma ce wanda ake kara na biyu, Meco, ya karbi kadarorin, da sanin cewa an sace su ne.
A cewar sa, laifukan sun ci karo da sashe na 280(2) da 328 da 411 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.
Wadanda ake tuhumar dai, sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.
Alkalin kotun, Mrs K.A. Ariyo, ya bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi Naira 200,000 kowanne, tare da tsayayyu biyu kowannen su. Kuma ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Mayun shekarar 2022.