Asusun sashen dake kula da tallafin kanana yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF ta yi alkawarin tallafawa gwamnatin jihar Kano ta Dk. Abdullahi Umar Ganduje domin ganin kowanne karamin yaro a jihar ya samu ilimi.
Wannan alkawarin tallafin ya fito ne daga bakin Dk. Euphrates Efosi Wose wato shugabar sashen ilimi ta UNICEF din, a yayin taron kwana biyu na masu ruwa da tsaki a kan harkokin ilimin kananan makarantu da Sakandare wanda ya gudana a ranar Talata a garin Kano.
UNICEF din ta tabbatar da cewa; shi wannan tallafin ya zama wajibi ne duba da yadda yake hakki ne a ilmantar da kananan yara. Sannan ta tabbatar da cewa; za su ba da wannan tallafin ne domin tabbatar da cewa kowanne yaro a jihar ya samu damar samun ingantaccen ilimi domin taimakon kawukansu.