Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta cimma yarjejeniya kan sayen dan wasan gaban Brazil Antony daga Ajax.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kungiyar kwallon ƙafan ta kasar Ingila ta sanar da hakan ne a yau Talata.
Ajax dai ta amince da cinikin Euro miliyan 95, kuma kuɗin zai iya tashi zuwa Yuro miliyan 100.
KARANTA ANAN: Muna Allah Wadai Da Zuƙi Tamallen Ministocin Buhari – ASUU
Antony ya zura kwallaye 31 a wasanni 134 da ya buga wa Ajax da Sao Paulo, da kuma kwallaye biyu a wasanni tara da ya buga wa Brazil.
A wani labarin kuma: Kotu Ta Sake Tsare Abba Kyari Bayan Ƙin Amincewa Da Bukatarsa
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da sabuwar bukatar bayar belin da DCP Abba Kyari da aka dakatar ya daga aikin.
Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke, ya ce Mista Kyari bai bayar da isassun dalilan da za a amince da bukatarsa ba, don ganin an bada shi a hannun beli.
Alkalin ya ce dan sandan da ake tsare da shi ya kasa kawo sabbin bayanai a sabuwar bukatarsa bayan an ki amincewa da bukatar belin da aka yi masa a baya.
Sakamakon haka Mista Nwite ya dage sauraron karar har zuwa ranar 19, 20 da 21 ga watan Oktoba domin ci gaba da shari’ar.