By Abbas Yakubu Yaura
Uwargidan gwamnan jihar Abia, Misis Nkechi Ikpeazu, ta gina katafaren rumfunan kasuwa mai dakuna 20 kowannen su tare da tsaftataccen ruwan sha a Ahiama Obete Ukwu Ibeme, Ahia Eke Amaude dake Onicha Ngwa da wata rumfar kasuwa a Umuohia, Ahiaba duk a Karamar hukumar Obingwa.
Matar gwamnan tace Manufar gina kasuwar shine don haɓaka ayyukan kasuwanci ga ‘yan kasuwa da abokan ciniki.
Misis Ikpeazu ta ce sha’awar mijinta ita ce ta samar da yanayin kasuwanci da ya dace da matan Jihar Abia; don tallafa wa tattalin arzikin iyalansu, don ƙarfafawar da aka ba wa ’yan kasuwa na gida a kowace kasuwa da aka gina.
“Mun bayar da tallafi ta hanyar tsarin lamuni na AWADEC kamar yadda gwamna ya amince da shi. Wannan tsarin rancen ba shi da ruwa amma ana sa ran masu cin gajiyar za su biya lamunin domin wasu su samu damar shiga asusun,” inji ta.
Don haka ta shawarci matan da su yi amfani da kayan aikin, su kula da lafiyarsu yadda ya kamata, sannan su tabbatar da cewa sashen na su ya je a yi gwajin jinsin halitta kafin a yi aure, don guje wa haihuwar ‘ya’ya masu ciwon sikila.