Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa, Hajiya Silifat Abdullahi Sule ta yi kira da a hada kai don cigaban yankin Arewacin kasar nan.
Ta yi wannan kiran ne a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin Jam’iyyar Matan Arewa na jiha a ofishinta da ke gidan gwamnati a Lafia ranar Alhamis.
Silifat Sule ta cigaba da cewa, tare da jajircewa da gaskiya, matan arewa suna da dukkan abun da ya kamata wajen tarbiyyar al’umma masu zuwa tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban yankin.
Uwargidan gwamnan ta kuma yi kira ga mata a matsayinsu na uwaye da su tabbatar da tarbiyyar ‘ya’yansu yadda ya kamata domin samun shugabanni nagari a nan gaba, kamar yadda ta yi Allah-wadai da yawaitar shan miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u a cikin al’umma.
Da take jawabi tun da farko, shugabar tawagar kuma babbar sakatariyar dindindin a jihar, Hajiya Sa’adatu Agede, ta bayyana cewa tawagar ta je ofishin ne domin bayar da goyon baya ga gwamnatin jihar a kokarinta na tabbatar da dorewar hadin kai da zaman lafiya a jihar. .
Sa’adatu Agede ta sanar da uwargidan gwamnan cewa kungiyar wadda ta samo asali ne tun zamanin Sir Ahmadu Bello, an farfado da ita ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da nufin samar da murya ga matan Arewa.
Ziyarar ta hada da gabatar da takardar nadi ga uwargidan gwamnan a matsayin uwar kungiyar a jihar.