By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayar da tallafin karatu ga wata dalibin da taci maki tara (9A’s) a jarrabawar kammala makarantar sakandare ta shekarar 2020,mai suna Confidence Nwozuzu.
Nwozuzu wanda ta fito daga karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar ta samu tarba daga Uzodinma a gidan gwamnati dake Owerri.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa jihar za ta ci gaba da sanin fitattun ‘yan asalin jihar.
Uzodinma yace, “Za mu ci gaba da gane da kuma karfafa gwiwar ‘yan Imola dake kawo martaba ga jihar ta hanyar banbance su ta hanyoyi masu ban mamaki.Confidence Chinaza Nwozuzu daga karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo ta samu karramawa ga jihar sakamakon bajintar data yi na samun maki mafi girna na (9As) a jarrabawar kammala Makarantar sakandare ta shekarar 2020.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “A saboda godiya da wannan rawar da ta taka, na umarci kwamishinan ilimi data tabbatar da daukar nauyin karatun Miss Chinaza ta hanyar aikinta zuwa matakin ilimi da ake bukata.
“Saboda haka, ina ƙarfafawa sauran ’ya’ya maza da mata na Jihar Imo dasu kara himma da jajircewa wajen neman ilimi shi ne babban abin ƙarfafawa don ci gaba a nan gaba.sannan ina taya Confidence Chinaza Nwozuzu murna.