By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan kasuwar da aka sace a kasuwar Kagara dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, wadanda suka yi garkuwa da su sun sako su bayan shafe watanni uku a hannun su.
Idan dai ba’a manta Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘Yan bindigar sun kai hari kan ‘yan kasuwa yayin da suke kan hanyar su ta dawowa daga kasuwar Kagara a ranar 9 ga watan Satumba, 2021, kuma sun yi garkuwa da mutane akalla 34.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da sakin mutanen da aka sace.