Shugaban Kamfanin ‘Peugeot Automobile Nigeria (PAN),’ Alhaji Ahmed Wadada, ya ba da gudummawar shinkafa, Taliyar Indomie, katifa, ruwa, sabulu da tsabar kudi ga marayu uku a garin Karu kusa da Abuja a ranar Litinin.
Karamar hukumar tana iyaka ne tsakanin jihar Nasarawa da Birnin Tarayya Abuja.
Wadada, wanda ya kafa Keffi Polo Ranch, ya ce kayan da aka bayar na cikin kuɗin da aka samu na Gasar Keffi Polo Ranch ta shekarar 2021.
Gidajen marayun da suka amfana sune Divine Mercy, Tudun Wada, Honor Orphange Home, Auta Balefi da God Love Foundation, Nyanya Gwandara, duk a jihar Nasarawa.
Wadada ya ce kudaden gasar wasannin Polo an sadaukar da su ne ga ilimi da kuma biyan bukatun marayu a cikin al’umma.
Ya bukaci masu hannu da shuni da ‘yan Nijeriya da su rika yin la’akari da halin da kananan yara masu rauni ke ciki.