Kusan mutane 29 ne suka kara rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa yayin da ruwa ke ci gaba da mamaye al’umma a sassan jihar.
Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu a irin wannan yanayi zuwa 92, in ji hukumomin ‘yan sanda a jihar da ke arewa maso yammacin kasar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawal Shiisu, ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Lahadin nan.
A cewarsa, mutuwar ta faru ne sakamakon nutsewa a ruwa, da kifewar kwale-kwale, da tsawa, da rushewar gine-gine.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ambaliyar ruwa na ci gaba da yin barna a jihar Jigawa yayin da al’ummomi da filayen noma suka samu illa a yankuna da dama na jihar.
Akalla mutane 83 da suka hada da yara da mata ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar tun daga farkon watan Agusta zuwa yau.
Ambaliyar ta kuma yi illa ga ababen more rayuwa a jihar, yayin da wasu tituna suka farfashe sakamakon zaizayar kasa, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin neman wasu hanyoyin da za su bi.
KARANTA KUMA:
Wannan halin da ake ciki yanzu ya sa daruruwan mazauna wurin yin gudun hijira, inda da dama suka yi zaman wucin gadi a gine-ginen jama’a.
A yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu, gwamnatin jihar ta yi alkawarin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa, yayin da ta yi kira ga jama’a da su kuma taimaka wa wadanda lamarin ya shafa da abinci da sauran kayayyaki domin dakile illar ambaliyar.
A makon da ya gabata ne hukumar kula da madatsan ruwa ta Najeriya NIHSA ta tabbatar da jihar Jigawa a matsayin jihar da ta fi fama da matsalar ambaliyar ruwan da ya addabi sassan kasar nan.
Ta ce kananan hukumomi 16 na jihar ne lamarin ya shafa sannan sama da mutane 72 ne suka mutu tare da lalata dukiyoyi, rayuka da kuma ababen more rayuwa a ranar 7 ga watan Satumba.
A yayin da ake samun karuwar mace-macen, hukumomi a jihar sun yi alkawarin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa tare da yin kira ga masu hannu da shuni da suma su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa da abinci da sauran kayayyaki domin dakile illar ambaliyar.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Anambra Ta Haramtawa Mata Sanya Gajerun Siket A Dukkannin Makarantun Jihar
Gwamnatin jihar Anambra ta haramtawa mata sanya kananan kaya a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da makarantun jihar za su ci gaba da gudanar da sabon zaman zangon karatu a ranar Litinin mai zuwa.