Cibiyar dake dakile cutuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta bayyana cewa an samu sabbin mutum 129 da suke dauke da cutar koron a kasar, wanda hakan ya sanya masu dauke da cutar adadinsu ya kai 162,891 a fadin kasar.
NCDC sun bayyana hakan ne a ranar Laraba a shafinsu na Twitter.
Ya zuwa yanzu adadin wadanda aka yi wa gwajin cutar a Nijeriya sun kai 1,767,694 tun bayan barkewar cutar a ranar 27 ga watan Fabarairun 2020. Inda kuma cutar a ranar Laraba din aka samu mutum daya da cutar ta kashe, wanda wannan ya sanya adadin wadanda cutar ta kashe suka kai 2,057 tun bayan bullar cutar a Nijeriya.
Cibiyar ta ce sabbin masu cutar a ranar Laraba sun fito ne daga jihohi 12 na kasar ciki kuwa harda birnin tarayya Abuja.
Inda daga cikin mutum 129 da suka kamu da cutar sun fito ne daga Legas inda take da 46, Ondo 19, Nasarawa 14, Kaduna 11, Borno 9, Bauchi 8, Akwa Ibom 5, FCT 5, Jigawa 4, Filato 3, Bayelsa 2, Osun 2 da Rivers 1.