Wadanda gobarar ta shafa a babbar kasuwar Mokwa ta jihar Neja, sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki bayan sun yi asarar kayayyaki da kadarori na miliyoyin naira.
Da take magana da gidan Talabijin na Channels, wata Toyin Abinbola mai sayar da kayan abinci ta ce ta yi asarar komai a wutar da ta tashi.
Wani dan kasuwa, Mutari Abiola, ya yi kira ga gwamnatocin kananan hukumomi, jiha da tarayya da su kawo musu dauki domin su sake fara sana’o’insu.
Tawagar gwamnatin jihar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Ahmed Ketso, ta kai ziyarar jaje ga shugaban al’ummar da aka fi sani da Ndalele Mokwa, Mohammed Shaba, wanda shi kuma ya bukaci a ba shi motar daukar kaya da sauran ababen more rayuwa a kasuwar domin gaggauta daukar mataki. idan aka samu faruwar makamancin haka a nan gaba.
Ketso wanda ya kuma jajanta wa wadanda abin ya shafa da kuma mutanen Mokwa ya bukace su da su kula da musabbabin aukuwar gobara domin kaucewa sake afkuwa a nan gaba.
A halin da ake ciki, Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Inga, ya bayyana cewa ana ci gaba da tantancewa da bincike don gano musabbabin tashin gobarar da kuma yawan asarar da aka yi.