Adadin wadanda suka mutu a ginin da ya ruguje a ranar Litinin a Ikoyi, na jihar Legas ya karu zuwa 42 a ranar Asabar, yayin da wadanda suka tsira kuma suka karu daga tara zuwa 15.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan yayin da yake bayar da karin haske kan lamarin.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu suka ziyarci wurin.
Sanwo-Olu, yayin da yake bayar da bayanai kan aikin bincike da ceto a wurin, ya ce, an ceto karin mutane shida kuma sun fara karbar magani a asibitin ‘yan sanda da ke Falomo na yankin, Ikoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalibai Mata Uku Sun Jikkata Yayin da Gobara ta tashi a Jami’ar Maiduguri
Wadanda suka tsira da ransu na baya-bayan nan su ne wata mace mai shekaru 38, Mai suna Glory Samson; da Ndajor Ahmed, Yunusa Abubakar, Ajiboye Habib, Jeremiah Samson, da kuma wani mutum mai suna Emem.
Yayin da akasarinsu suka samu raunuka daban-daban, Samson, mai shekaru 20, an ce yana cikin suma.
Sanwo-Olu ya ce iyalai 49 ne suka cika rajistar ne man wadanda suka bata tun da safiyar Asabar