Duk da sassauta dokokin kulle da Shugaba Buhari ya yi daga ranar Litinin mai zuwa, hukumar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta umurci ma’aikatan da ke zaune a wajen birnin da ka da su dawo wurin aiki a yanzu.
Wannan umurni yana kunshe ne a wata sanarwa da Ministan Abuja Mallam Muhammad Bello ya fitar ranar Asabar, inda ya ce za a aiwatar da matakin sassauta dokar ne sannu-sannu.
Sanarwar ta kara da cewa dukkanin taruka haramun ne a birnin da suka hada da na biki da addini.
Har wa yau, wuraren taruwar jama’a kamar gidajen kallo da sinima da wasanni da shakatawa da na shan barasa, baki daya za su ci gaba da kasancewa a rufe.
Game da sufuri kuwa, an haramta yin acaba ko okada a fadin Abuja, sannan ‘yan tasi mutum uku kacal za su dauka bayan direba, yayin da ‘yan adaidaita sahu za su dauki mutum biyu ban da direba. Su ma motocin bas za su dauki kashi 50% ne kawai na abin da ya kamata motar ta dauka kamar yadda rahoton BBC Hausa.