Wani Dan Nigeria Mai suna Bright Ben ya koka kan yadda wani Malamin Majami’ar shi, Mai suna Moses Adeeyo, ya aure masa matar shi mai Muna Tina Adeeyo “Bisa umarnin wahayi da a ka yi ma shi”
Faston ya bayyana cewa, ya auri Tina Adeeyo ce, bisa “Umarni da ya samu da Ubangiji” a cewar shi.
Lokacin da ya ke nuna bacin ransa a shafin sa na Facebook Bright Ben ya bayyana cewa, Malamain majami’ar shi ya aure matar shi, bayan wani abokin shi ya tambayeshi meye gaskiyar lamarin abun da ya faru.
Bright Ben ya ce, Faston shi ya aure matar shi, bisa wahayi da a ka yi mashi.
Ya wallafa cewa, ” Faston Majami’a ta, ya aure mun mata sabida wahayi da a ka yi mashi” inji shi.
Bayan bayyana korafin shi a kafar sadarwa na Facebook, sai kanwar tsohuwar matar ta shi, Mai suna Elizabeth Okonkwo ta gargade shi da ya yi gaggawar cire rubutun, ko kuma ta tona Mai asirin abubuwan da ya yi mata a fadin duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dangin mujine su ke kashe mana aure, inji Ummi Gombe
Kazalika Elizabeth ta mayar wa mutanan da ke sukar auren da cewa, Yar uwarsa ta fita daga ukubar wahalar da take ciki.
Daga cikin kalaman ta, Elizabeth nuna cewa, Bright Ben ba miji na gari ba ne, hakan na daya daga cikin daliban da sukasan Tina ta bar gidan Tsohon mijin ta.
Moses Adeeyo babban Malamin mujami’a ne a cocin Word Bank Assembly International Church, ya auri Tina ce bayan ya saki tsohuwar matar shi.
Comments 1