Tun da aka soma sauraren karar da Atiku na PDP da Buhari na APC, kan kalubalantar nasarar da Buhari ya samu, Shugaban Hukumar zabe na kasa ke ta maganganu masu karo da juna.
Idan an gabatar da hujja, sai ya yi ta Jayayya. Amma daga karshe kuma a gano shi ne ba shi da gaskiya.
Wasu misalai guda biyu: PDP ta ce INEC tana da rumbun tattara bayanai, shi kuma Shugaban INEC ya ce babu. Amma daga baya wasu ma’aikatan INEC sun zo sun bada shaida cewa akwai rumbun. Har ma an koya musu yadda za su yi amfani da shi
Kan batun jihar Zamfara, Kotun sauraren karar ta bukaci Shugaban Hukumar zaben ya gabatar da wadansu takardu. Amma Shugaban na INEC yana ta jan kafa. Har sai da kotu ta tilasta masa lallai ya kawo takardun.
To wai shin me ya sa Shugaban Hukumar zaben na kasa ke maganganu masu karo da juna?
Me ya sa yake jan kafa wajen gabatar da duk takardun da ake BuKata? Ai ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi.