• Wajibi ne Kowani Dalibin Sakandare a fadin jihar Kano ya Mallaki Lambar Zama Dan Kasa wato NIN.
• Kwamishinan Ilimi na jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Alhamis a garin Kano.
• Ya ce Hakan zai taimaka wa ma’aikatar Ilimin jihar domin samu dukkanin bayanan Dalibai Kuma hakan zai kawo sauki a fannin magudin jarabawa.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, dole ne dukkan daliban makarantun sakandiren gwamnati da ke fadin Jihar su mallaki Lambar shaidar zama dan Kasa wato (NIN).
Kwamishinan Ilimi na jihar na jihar, Malam Sanusi Sa’id Kiru wanda ya sanar da hakan ya yin da ya ke ganawa da manema labarai a Kano, a jiya ranar Alhamis.
Ya ce umarnin ya hada da daliban matakin ajin karamar sakandire na farko wato (JSS 1), harzuwa ajin babbar sakandire na karshe wato (SS 3).
A cewar shi, an bullo da matakin ne, domin a sami damar tattara cikakkun bayanan daliban da ke fadin Jihar, domin saukaka wa gwamnati wajen tsare-tsare, kasafin kudi, da kuma rage magudin jarrabawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gaskiya da Adalcin Buhari ya sa na koma APC inji wani Gwamna
Kwamishinan ya kuma ce, shirin zai taimaka wa Ma’aikatar shi, ta kara samun bayanai ta hanyar daukar zanen yatsu goma, da kuma hoton Fasfo, da kuma sa hannun kowanne dalibi.
Daga nan sai ya yi kira ga Hukumar da ke Kula da Manyan Makarantun Sakandire ta Jihar (KSSSMB) da ofisoshin ilimi na shiyya-shiyya da shugabannin makantu da daraktoci kan su tabbata an aiwatar da umarnin kamar yadda ya dace.
A karshe Malam Muhammad Kiru ya kuma ce, tuni ma’aikatar shi, ta kammala shiri da ofishin Hukumar Kula da Shaidar Zama dan Kasa (NIN) da ke Jihar Kano, domin saukaka wa daliban mallakar lambar a matakin shiyya-shiyya.