
Wakilan Fulani daga Kananan Hukumomin Kebbi sun kawoma Gwamna Bagudu ziyara
Sarakunan Fulani dake kananan hukumomin ashirin da uku dake Jahar Kebbi sun kawama Gwamnan Kebbi Ziyarta kan batun sace Dalibai da’akayi a Makarantar Sakondari dake Yawuri a Jahar.
Bello Aliyu Gotomo Shugaban Fulani dake Jahar ya bayyana ma gwamna da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zasu bada gudummawa wajan kawar da ta’addanci dake damun Jahar.
KARANTA:-Hukumar Kasar Dubai sun haramta zirga-zirgar Jirage daga Najeriya
Mr. Gotomo yace ” Kabilar Fulani sun tsani ta’addanci Kuma fulanin dake da hannu cikin ta’addanci makiya Fulani ne sannan makiya kasar Najeriya ne.
Yace Fulani kabila ne masu son zaman Lafiya sannan duk wadanda ke da hannu Allah ya tsine masa a duk inda yake a fadin kasar nan.
Ya Kara da cewa Fulani masu wannan ta’addanci suna kara fata sunan kabilar ne wadanda tun can da an san sune da noma da kiwo.
Yace sun zo wannan ziyarar ce don nuna goya bayansu na cigaba da yaki dasu don samu a kubutar da sauran daliban da aka kwashe.
Gwamna Bagudu yace wannan ziyara ce mai muhimmanci wadda zata karfafama Jahar wajan dakile dukkanin ta’addanci da tabbatar da duk wani Dan taadda bashi da wurin zama a gaba daya Kananan Hukumom ashirin da daya a Jahar.
Major Rabi’u Kamba mai ba gwamna shawara kan harkar tsaro ya nuna godiyarsa da yabama kungiyoyin fulani da suka nuna goyon bayansu don ganin an dakile ta’addanci dake faruwa a Jahar.