By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kama wani mutum mai suna Moses Oko, dan shekara 20 da ake zargin yaron Yahoo ne da laifin kashe wata daliba mai matakin karatu na 300L dake jami’ar UNIJOS, Jennifer Anthony, wadda aka gano gawarta a ranar 1 ga watan Janairu, 2022.
An gabatar da wanda ake zargin ne tare da wasu abubuwan da ake zargin an aikatawa marigayiyar ta’asar tare da wata takarda mai shake da jini da kuma cokali mai dauke da jini da ake zargin an yi amfani da su wajen fizge idon marigayiyar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bartholomew Onyeka wanda ya kama Moses Oko, tare da sauran wadanda ake zargi da aikata wasu manyan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da kuma kisan kai, ya bayyana cewa an kama Oko ne a ranar Talata, 11 ga watan Janairu a jihar Benuwe.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Jos, CP, ya ce, “Rundunar ta hanyar jagorancina ta hada dabaru da dama don dakile aikata laifuka a jihar Filato. Amma a duk lokacin da aikata laifi ya faru, muna yin duk ƙoƙarin da muke da shi na kama masu aikata laifin domin su fuskanci sakamakon ayyukansu na laifi.
“Bayan kisan gillar da aka yi wa Miss Jennifer Anthony, dalibar jami’ar Jos mai matakin karatu 300 wadda aka tsinci gawarta a ranar 01/01/2022 a Domus Pacis Guest House, Jos da wani mai suna Moses Oko ‘m’ mai shekaru shekaru 20, wanda ake zargin saurayinta ne da ya gudu bayan ya aikata laifin, rundunar ‘yan sandan a yunkurinta na cafke wanda ake zargin, ta fara farautar wanda ake zargin tare da bin hanyarsa zuwa jihar Benuwe inda jami’an ‘yan sanda masu ido da ido suka kama shi. Umurni Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.”