Sheikh Mallam Isah Ali Ibrahim Pantami
Yanzu yana da digiri na uku a ilmin na’ura mai kwakwalwa, shine Malami matashi na farko a tarihin duniya daga nan Nigeria wanda jami’ar Musulunci dake garin Manzon Allah (SAW) ta daukeshi aikin karantawar, saboda ya cika dukkan sharadin da suke nema
Wasu suna ganin cewa ai yanzu Malam kudi yake samu saboda shugaba Buhari ya bashi mukamin Director General a ma’aikatar NITDA shiyasa wai yake yin shiru akan matsalolin Nigeroa, wai an toshe bakin malam, ni kuma nayi imani da Allah abinda Malam yake samu a jami’ar Madina baya samu anan Nigeria, to bari kuji, yau ta kama zan fadi wata magana
Malam yace “Dole fa a taimaki shugaba Buhari, wannan itace damar da ake da ita kafin ta kubuce, duk wanda zai taimaki shugaba Buhari yayi don Allah kawai, Malam yace wallahi tallahi abinda yake samu a jami’ar Musulunci ta Madina ya ninka sau uku na abinda yake samu a matsayin da shugaba Buhari ya bashi.
Haka Malam ya tabbatar da haka da bakin sa, Taimakon shugaba Buhari ne ya dawo da Malam gida Nigeria, amma abinda yake samu a jami’ar Madina ya ninka abinda yake samu sau uku anan Nigeria, amma haka ya hakura ya dawo gida domin ya bautawa kasarsa ya kuma taimaki shugaba Buhari wajen gina mana sabuwar Nigeria
Don haka mai zagin Malam Isah Ali Pantami, Malam bazai saurari irin hayaniyar ba, ba Kuma zai mayar da martani was wannan shirirtar ba.
Allah Ka taimaki Dr Isah Ali Ibrahim Pantami, Allah Ka tsare shi daga dukkan sharri da batancin masu batanci da mahassada.