- Wani dan Najeriya mai hazaka a jihar Legas ya kera mota mai kama da babur mai ƙafa da kuma ƙaramar motar bas don jigilar jama’a
- Mutumin ya bai wa mutane mamaki lokacin da ya bayyana cewa ya yi amfani da injin keken lantarki ne ya sa motar ta yi gudu
- ‘Yan Najeriya da suka kalli bidiyon nasa sun ce yana da hazaƙa ta hanyar kirkire-kirkirensa, kuma mutane irinsa suna buƙatar a tallafa musu
Wani mutum a unguwar Sagamu da ke jihar Legas ya ba mutane mamaki da motar da ya kera da kansa.
Motar ta yi kama da keke mai ƙafa uku (keke) daga nesa.
Hakanan yana da jikin keke. Amma ba kamar ta ba, motar tana da ƙafafu huɗu da sitiyari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ta Kammala Karatu Da CGPA 1.0, Hakan Yasa Take Kuka Har Da Burgima.
Mutumin da ya tuka motar ya tabbatar da cewa ya kera ta, ya kuma kara da cewa ya haɗa motar lantarkin da injin keken lantarki.
Mutumin ( @him_oba_ifagbaiye ) wanda ya yi masa tambayoyi a cikin faifan bidiyo na TikTok da aka wallafa ta yanar gizo ya yi mamaki.
Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun ce hakika ‘yan Najeriya suna da hazaƙa.
Motar tana da faɗin da zata iya ɗaukar fasinjoji masu yawa kamar ƙaramin bas na yau da kullun.
Mutumin mai hazaƙar wanda ya kera mota mai kama da keken ya bawa masu amfani da yanar gizo mamaki sosai
Majiyarmu ta tattaro wasu daga cikin martanin da akai kamar yadda suke a kasa:
@Doyen ya ce: “Kwarai kuwa.”
@jaiyeola05 ya amsa da cewa: ” Da sake fa! Kuɗin injin keken lantarki fa yana da tsada.”
@ABDULKABIR ya ce: “Baba Ajara yana da hazaƙa da ya kamata nayi wannan bidiyon tun da farko.”
@Bee_ Jay ya ce: “Ta yaya zamu kira wannan.”
@IstoLee ya ce: “ku ƙara yaɗa masa bidiyon nan don Allah.”
@Ayinde ya ce: “Sunan ta Limourope.”
@Yomiking ya ce: “Gaskiya Najeriya tana da Haziƙai, ku yi iya kokarinku don taimaka musu don Allah, ba za ku taba rasawa ba da yardar Allah.”
@MIDE ya ce: “A’a wannan ai G Wagon zata zama.”