Wani Sufeto na Ƴan Sanda Micheal Timitimi Wanda yake aiki a Rundunar Ƴan Sandan Jahar Bayelsa a ƙarshen hutu ya faɗi, ya mutu a lokacin binne Kakar shi a Al’ummar Igbedi na Ƙaramar Hukumar Kolokuma/Opokuma ta Jahar.
Marigayi Sufeto ɗin yana aiki a wani ofishi na Ƴan Sanda, kafin mutuwar shi.
Shugaban Yan Sintiri na Jahar Bayelsa Mr Oyinkuro Lucky Asanakpo yakai ziyarar ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa Sufeto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jahar Filato ta bankaɗo Ma’aikata Masu ritaya da Matattu 413 dake karɓar Albashi
Dayake jawabi a lokacin ziyarar ta’aziyyar, Asanakpo ya bayyana yadda Marigayin ya ziyarce shi a ranar Alhamis data gabata, domin gaya mashi akan mutuwar Kakar tashi, tare da gayyatar shi zuwa Binne ta.
Wani wanda ya shaida lamarin ya bada rahoton cewa ya faɗi ne ya mutu, jim kaɗan bayan yayi rawa domin girmama Kakar shi.
A ziyarar da aka kai, anji cewa Ɗan sandan ya bar wurin aikin shi, tare da tafiya cikin ƙwalla, bayan yaji cewa ɗan sandan ya mutu.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Bayelsa SP Asinim Butswat Wanda ya tabbatar da mutuwar Jami’in, yace dama yana da matsalar rashin lafiya, kuma ya rasu a Asibiti, inda aka kaishi bayan ya faɗi ƙasa.