Wasan sada zumunta da wasannin gasa tsakanin ƙasashen Denmark da Ingila yana zuwa da abin mamaki idan zasu fafata wasa a tsakaninsu koda ace wasan sada zumunci ko wasan wata gasa a nahiyar turai inda abin yake ɗaurewa mutane kai.
Domin yanzu shekaru 41 kenan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan na England da Denmark sun fafata wasanni guda 7 amma dukkaninsu duk ƙasar dazatai nasara to zatayi nasara ne daci 1 maiban haushi.
Ga jerin yadda haɗuwar tasu ta kasance tun daga 1979 zuwa 2020:
1. A shekarar 1979 sun haɗu inda England ta doke Denmark daci 1 da nema kuma ɗan wasan England wato Kevin Keegan ne ya jefa ƙwallon.
2. A ahekarar 1983 Denmark ta wanke England daci 1 da nema inda ɗan wasa Allan Simonsen ne ya jefa ƙwallon.
3. A ahekarar 1988 England ta lashe Denmark daci 1 da nema inda ɗan wasan England Neil Webb ne ya sami nasarar jefa ƙwallon.
4. Haka ma a 1990 England ta doke Denmark daci 1 mai ban haushi inda ɗan wasa Gary Linker ne ya jefa waccan ƙwallon.
5. Sannan a ahekarar 1994 ma England ya lashe Denmark daci 1 da nema inda ɗan wasa David Platt ne ya sami nasarar jefa ƙwallon.
6. Haka zalika a ahekarar 2014 ma England ta doke Denmark ta hannun ɗan wasa Daniel Sturrigde daci 1 da nema.
7. Sannan kuma a wannan ahekarar ta 2020 Denmark ta lallaaa England daci 1 mai ban haushi inda ɗan wasa Christian Eriksen ne ya sami nasarar jefa ƙwallon.