Masu iya magana sun ce inda ranka babu abinda ba za ka gani ba, kazalika kuma an ce na zaune bai ga gari ba.
Wannan maganganu na zuwa ne daidai lokacin da al’ummar jihar Bauchi suka wayi gari da wani abu mai kama da almara ko kuma mamaki inda wani aljani ya bayyana a jihar.
Cikin wata hira da manema labarai a birnin Bauchin Yakubu, aljanin mai shekara 1800 ya ce jinsun su na aljanu ba sa amfani da wayar salula, baya da aka tanbyae shi da ya cire makullin wata waya a matsayinsa na aljani.
Ko da yake kamar yadda aka camfa, an san aljanu da rikiɗa a ko da yaushe suka ga dama, amma wannan aljani mai suna Hayatuddeen ya sha banban da sauran, domin kuwa ko da aka bukaci ya yi hakan sai ya nuna Allanbaran cewa ba haka kawai ne aljani ke rikiɗa ba.
Ya kara da cewa yanzu baya ga shi, akwai ƙarin aljanu kimanin 99 da a ko da yashe yake yawo tare da su babu shamaki.
Sai dai wani babban al’amari da aka lura da aljani Hayatuddeen shine yadda ya bayyana cewa batun yiwa aljanu rukiya a fitar da su zance ne kawai, domin babu yadda za a yi aljani ya fita daga jikin mutum sai dai ya kwanta bayan an kwana biyu ya sake tashi.
Kuma hakan a cewarsa ba ya rasa nasaba da yadda suke da kyakkyawar dangantaka tsakanin su da bil’adama wanda take kaiwa ga suna zama yan uwa idan wuri ya yi wuri.
Idan aka yi la’akari da yadda al’umma ke neman kuɗi ido rufe a wannan zamani musamman a kasa Najeriya, yanzu haka idan aka bayyana Aljani Hayatuddeen a ɗaya daga cikin masu irin wannan bukata wata kila ba a yi karya ba, kamar yadda al’umma da dama a jihar ta Bauchi suka faɗi jim kaɗan bayan jin bayyanarsa.
Idan ba ku manta ba ko a baya mun kawo muku labarin wani mai suna Musa Karkum wanda ya bayyana kansa da Mala’ika, amma daga bisani dai ya koma mutum bayan da ya yi arangama da dakarun Hisba a jihar.
Yanzu dai abin jira a gani ga aljani Hayatuddeen shine yadda za ta kaya idan labarinsa ya bazama gari irin na wancan mala’ika, kana mu kuma za mu ci gaba da bibiyar lamarin muna kawo muku karin bayani.