Likitocin da ke aiki a Asibitin Barau Dikko sunyi Allah wadai kan yunkurin yajin aikin da Kungiyar likitoci ta (NARD), ke niyyar tafiya bayan gwamnatin tarayya ta ki amincewa da wasu kudirorinsu. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Dakta Sayyid Egbunu Muhammed, babban likita kuma shugaban kungiyar likitoci ta NARD dake asibitin, yace a matakin yajin aikin a Jaha kadai, su ba za su shiga yajin aikin ba, amma idan daga kasa ne baki daya to za su yi biyayya da umarnin.
Kamar yadda yace ” A matakin jaha, mudai ba za mu shiga yajin aiki ba, kuma wannan ba zai nuna cewar bama tare da kungiyar NARD ba ne, idan abun yaci tura to tabbas muma za mu fada cikin yajin aikin.”
KARANTA:- Gamayyar Kasashen Larabawa (UAE) ta tsawaita dokar da ta sanyawa Nigeria na zirga-zirga
Kamar yadda yace rashin cika wasu kudiri ne na likitocin wanda gwamnatin tarayya ta kasa cikawa ya janyo yajin aikin.
Ya roki gwamnatin tarayya da ta duba akan lamarin.
Wani daga cikin likitocin, Muhammad Auwal Musa, yace shi baima san da batun zuwa yajin aikin ba, inda wani likitan ke cigaba da kulawa da marasa lafiyansa.
Haka kuma a dakin jinyar yara, mun hango wani likita na koyar da wasu daliban likitanci wanda hakan na nuni ga yajin aikin bai kankama ba.
A wani labarin
An kaddamar da bada tallafin Taki ga manoma da ambaliya ya shafa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kaddamar da tallafin Taki ga manoma dubu uku da iftila’in ambaliya ya shafa a gaba daya jahohin kasar nan.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shine dai Jagoran gidauniyar samar da abinci, wanda mataimakinsa gwamnan Jahar Kebbi Atiku Bagudu, ya wakilce shi a yayin kaddamar da tallafin.
Ambaliyar dai ta zamo sanadiyyar rushe gidaje da gonakin jama’a gami da salwantar abubuwan daban-daban.
Buhari yace an amince da bada tallafin ne don ya rage radadin asarar da manoma suka tafka a lokacin da ambaliyar ta auku.
Shugaba Buhari yace wannan ya zo ne karkashin hukumar samar da tsaron abinci dake karkashin jagorancin nasa.
Yayi kira ga Yan Najeriya da su sanya ido wajan tabbatar da cewa tallafin ya isa ga hannun talakawa da wadanda abun ya shafa.
Kamar yadda yace ya kamata kungiyoyi ma su zaman kansu, da kafafen watsa labarai su taimaka don ganin kowa ya sami tallafin.
Daga cikin kayan da za’a rarraba wajan tallafin sun hada da kayan feshi, masara, irin shuka daban-daban, maganin feshi da sauran kayayyaki noma daban-daban.