Wani mai bishara da ke wa’azi a wuraren shakatawa na mota ya ƙi karbar hadaya da wata mata ta bashi yayin da yake wa wa’azin, Anonymoustales.net ta rawaito.
A wani faifan bidiyo daya wallafa a shafin TikTok a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba,anga mutumin ya ki karban naira 36 da aka ba shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Ya Bada Tallafin Miliyan 50 A Jihar Jigawa
Masu amfani da TikTok sun yi gaggawar mayar da martani ga bidiyon tare da da yawa daga cikinsu suna cewa bai kamata kudi ya zama manufar wa’azi ba.
Wani mai wa’azi a Najeriya da ke gudanar da wa’azinsa a wuraren shakatawa na motoci ya ki amincewa da tayin da wata budurwa ta masa na bashi sadakar Naira 36.
Mai wa’azin wurin shakatawar motocin na Najeriya ya dage cewa bayar da naira 36 ba kyauta ba ce. A cikin wani faifan bidiyo da @youngdrsmilecfr ya wallafa a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, an ga mai wa’azi yana jayayya yayin da ya ki kabar kudin da budurwar ta bashi.
Budurwar ta gaya wa mai wa’azi cewa Naira 36 kawai take da ita. Ya fusata yana nanata cewa irin wannan hadaya ta yi kadan da ba za a iya bayarwa ba.
Da yake magana da matar ta tagar motar bas din, bawan Allah ya ki karban kudin da yake ganin bai dace ba.
Bidiyon ya haifar da martani yayin da yawancin masu amfani da TikTok suka garzaya zuwa sashin sharhi don bayyana kalamansu.
A WANI LABARIN KUMA: Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Sun Bukaci Wani Taimakon Daga Gwamnatin Jiha
Mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a jihar Bayelsa sun koka da halin da suke ciki yayin da suke komawa gidajensu bayan da gwamnatin jihar ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar a hukumance.
Gwamnatin jihar Bayelsa ta bude sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin jihar a yayin da ake fama da ambaliyar ruwa a watan jiya. Gwamnati ta kuma samar da abinci da sauran muhimman kayayyaki a sansanonin ga wadanda abin ya shafa.