Wani sashe na wani bene mai hawa biyu da ake kan ginawa a Abuja ya rufta tare da wani mutum a cikinsa, da ya mutu har lahira.
Ginin da ya rushe yana bayan Rukunin gidaje na CITEC Estate da ke kan titin Airport, na yankin Jabi.
Lamarin, a cewar Darakta Janar (DG), Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya (FEMA), Alhaji Abbas Idris ya ce, ya faru da misalin karfe 1 na sanyin safiyar yau Laraba.
Idris ya shaida wa jaridar The Nation cewa, an ajiye gawar marigayin a cibiyar lafiya ta tarayya FMC dake yankin Jabi.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC ta nuna damuwa kan Matsalar Tsaro a Anambra
A cewarsa: “Wani sashe na ginin da ake kan ginawa a bayan Rukunin Gidaje na CITEC Estate da ke kan titin Airport, a jabi ya fadi” inji shi.
“Mutum daya ya mutu. Kuma an ajiye gawar shi a cibiyar kula da Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Jabi. Kuma lamarin Ya faru da karfe 1 na safiyar yau Laraba, an Kuma kwashe mutanen dake cikin ginin, zuwa wani wuri mafi aminci, don hana ƙarin asarar rayuka sakamakon ci gaba da tsagewa da ginin keyi ”. a cewar shi