By Abbas Yakubu Yaura
Wani ginin beni mai hawa uku ya ruguje a kan titin Ahmadu Belle Way dake kusa da dakin karatu na jiha a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa lamarin ya afku da misalin karfe 13:39 na ranar Alhamis 17 ga watan Maris.
DUBA WANNAN LABARIN: Hukumar NDLEA Ta Kama Masu Safarar Miyagun Kwayoyi 111 A Jihar Kaduna
Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
Saminu yace ofis din su da yake karbar kiraye kirayen kiran gaggawa ya samu kira ta hukumar sadarwar ta kasa NCC reshen jihar kano da misalin karfe 13:39 na rana inda ta sanar dasu faruwar wani Hatsarin ruftawar wani ginin beni mai hawa uku dake kan titin Ahmadu Belle Way Daura da dakin karatu na jiha.
Kakakin hukumar yace jami’an su sun isa wurin da hatsarin ya afku inda suka iske wani ginin beni mai hawa uku da ake tsaka da ginawa ya rufta.
Saminu yace iftila’in ya rutsa da wasu kafintoci da magina a lokacin da suke tsaka da aikin sai ginin benin ya rufto daga hawa na uku inda ya rutsa da ma’aikatan dake cikin wurin.
Kazalika yace tsautsayin ya rutsa da mutane da dama daga ciki akwai mutum biyu da abin yafi shafa akwai Danjuma Tijjani mai shekaru 52 wanda aka samu na sarar kubutar dashi a raye inda ya samu munanan raunuka, sannan akwai Rabi’u Musa mai shekaru 32 wanda aka ceto shi baya cikin hayyacin sa.
Sannan yace ragowar mutane da tsautsayin ya rutsa dasu wanda basu ji rauniba sun sami nasarar tserewa kafin zuwan jami’an hukumar kashe gobara wurin.
Ya kara da cewa dukkanni wadanda iftila’in ya rutsa dasu an garzaya dasu zuwa Asibitin Muhammad Abdullahi Wasai dan basu kulawar likitoci, inda daga baya aka tabbatar da mutuwar Rabi’u Musa sannan yace jami’an sa sun mika gawar sa a hannun jami’in dan sanda kofur Zilkifulu Sulaiman dake aiki a sashen ofishin ‘yan sanda na Nasarawa.
Saminu yace musabbabin faruwar lamarin har yanzu basu kai ga tantance waba.