By Abbas Yakubu Yaura
Wani Bishop na Wusasa dake cocin Anglican Bishop Ali Buba Lamido ya bada shawarar cewa ya kamata a kafa dokar ta baci a yankin arewacin Najeriya.
Hakan a cewarsa zai kawo karshen ayyukan ta’addanci da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane da suka mamaye yankin.
Bishop din ya yi wannan roko ne a sakonsa na Kirsimeti a lokacin da yake gabatar da wa’azi a Wusasa Anglican Diocese, a Zariya dake jihar Kaduna.
Sannan ya lura cewa halin da ake ciki na rashin tsaro a Arewa na ci gaba da zama abin ban tsoro da ban tausayi, don haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dauki kwararan matakai don dakile matsalar.
Bishop Lamido yace, “Duk da cewa gwamnatin tarayya na sa ‘yan Najeriya su yarda cewa tana samun nasara a yakin da ake yi da ‘yan bindiga, amma halin da ake ciki a kasa lamarin ya yi nisa sosai.”