Dr Emmanuel Kure, shugaban ‘Vision Pioneer and founder of Throne Room Trust Ministry,’ dake Kafanchan, a jihar Kaduna a ranar Lahadi ya bada tallafin kayayyakin abinci da ya kai na naira miliyan daya da dubu dari biyar ga wadanda suke gudun hijira da hare-haren bayanan ya shafe su a Kudancin Kadunar.
Kure ya bayar da tallafin ne ga ‘yan gudun hijirar da suke sansanin Zonkwa dake karamar hukumar Zango Kataf a jihar.
John Apata, wanda shi ne shugaba mai kula da kasashen duniya na gidauniyyar, shi ne wanda ya wakilci Kure, inda ya ce sun bayar da tallafin ne a wani mataki na rage radadin talaucin da marasa galihu ke fuskanta.