By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da laifin yiwa wata mata ‘yar shekara 22 fyade a Abeokuta, babban birnin jiha.
DUBA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Mace Ta Farko A Matsayin Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka
Lamarin ya faru ne a Eleweran, Abeokuta, inda a ranar Larabar da ta gabata ne wani matashi mai suna Seun Orokunle, mai shekaru 38, ya gayyaci abokinsa Sarumi Sodiq, don ya yi wa masoyinsa fyade.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Oyeyemi ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafin da wanda abin ya shafa ta kai ofishin karbar korafe-korafen jama’a da ke Eleweran, Abeokuta.
Kakakin ‘yan sandan ya rawaito wanda abin ya shafa ta ce da isa gidan masoyin nata, ta shiga bandaki ta yi wanka, kuma ba ta sani ba, Orokunle ya gayyaci abokinsa da ya zo kai tsaye ya same ta a bandaki, sannan ya fito da ita. Biyu daga cikinsu sun koma yin lalata da ita bayan sun yi mata duka.
PPRO ya ce, “Bayan gamsuwa da kansu, sai saurayin nata Seun Orokunle ya dauki kayanta ya tsoma su a cikin bokitin ruwa domin kada ta bar gidan nan take.
“Ta kuma kara da cewa mutanen biyun wadanda suka yi ikirarin ‘yan kungiyar asiri ne, sun yi barazanar kashe ta idan ta kuskura ta kai rahoto ga kowa.”