By Abbas Yakubu Yaura
Wani babban dalibi a kwalejin ilimin addinin musulunci ta Elkanemi dake Maiduguri ya tsaga makogoro wani karamin daliba mai suna Jubril Mato dan shekara 11 a kwalejin tauhidin addinin musulunci.
Karamin dalibin mai suna Jubril, wanda a halin yanzu yake kwance a sashin kula da lafiya na asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, a cewar rahoton, babban dalibin ne ya hukunta shi saboda ya ki gudanar dayi masa aiki.
“Babban abokin aikin sa, wanda yake a ajin SS2, ya aika Jubril ya yi masa wani aiki, amma bai je ba. A cikin wannan daren mai tsanani, ya zo ya dauke shi ya kai shi wani wuri mai natsuwa inda ya yi amfani da reza ya yanke masa wuya sosai, wanda hakan ya yi sanadin raunata yawancin jijiyoyin wuyan sa da kuma hanyar numfashin sa.” a cewar Wata majiya daga makarantar.
Babban dalibin, a cewar majiyar, wanda hukumomin makarantar suka boye sunansa, ya bar wanda lamarin ya rutsa dashi cikin halin rai kokai jike da jini. Bayan wasu mintuna Jubril yayi fama inda ya kai kansa ofishin shugaban makarantar kafin daga bisani ya fadi ya suma.
An garzaya da Jubril zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri kuma an kwantar da shi a cikin mawuyacin hali a sashin kula da lafiya. An kama wanda ya aikata laifin, wanda aka ce an cusa masa wasu abubuwan da suka shafi tunanin mutum daga bisani aka mika shi ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike.
Lamarin, a cewar majiyar, ya faru ne a ranar Asabar 16 ga watan Janairun 2022 amma hukumar makarantar ta boye shi da nufin nisantar da jama’a.
Wanda iftila’in ya rutsa dashi Jubril, an ce dan marigayi Mai shari’a Sadi Mato ne na babbar kotun tarayya ta jihar Kano, kuma mahaifiyarsa Hajiya Aisha ta sake auren wani babban ma’aikacin gwamnati a jihar Yobe.
Sai dai kuma abin takaicin ‘yan uwan wanda lamarin ya rutsa dashi , sabon mijin A’isha, (Kaban Jubril), wanda hukumar makarantar ta kira su jim kadan bayan faruwar lamarin, ya hana wanda lamarin ya faru da su da mahaifiyar sa kai rahoton harin ga ‘yan sanda.
Wani ma’aikacin kwalejin, wanda shi ma ya zanta da ‘yan jarida ya tabbatar da cewa, batun Jubril Mayo ba shi ne na farko ba domin an sha samun irin wadannan abubuwa da dama da suka faru a kwalejin amma mahukuntan makarantar sun ci gaba da boye abubuwan da suka haifar da karuwar laifin.
“Wannan ba shi ne karon farko da ake samun tashin hankali da makami a kwalejin ba. Akwai wasu kararraki da dama da suka shafi cin zarafi da makami, amma hukumar makarantar ta share ta a karkashin kafet. Wannan na nufin muna kara haifar da wasu wadanda abin ya shafa sakamakon gazawar da muka yi,” in ji malamin.