Wani dalibi mai matakin karatu aji na biyar, (Level 500) dake karatu a jami’ar Michael Okpara ta nazarin aikin gona Umudike, MOUAU, a jihar Abia, mai suna Modestus Hyacinth Egbulefu, ya kashe kansa bayan ya sha kwaya a unguwar Ikwuano, dake jihar.
Egbulefu, wanda dalibi ne a sashen Injiniyancin Lantarki an ce yayi tsallake ne daga wani bene mai hawa 3 da aka bayyana sunansa da ango Base Lodge, bayan ya sha ya bugu sosai.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:40 na safe yayin da sauran daliban abokan karatunsa suka kadu da samun labarin abinda ya faru.
Majiyoyi sun shaida cewa, bayan fadowar tasa, nan take ya mutu kafin a kai shi, zuwa asibiti don bashi kulawar gaggawa.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa an ajiye gawarsa a wani dakin ajiyar gawa da ba a bayyana ba a yankin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin martanin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna, ya ci tura.
An kira shi a waya bai samu dagawa ba, kuma an aike masa da gajeren sako, har yanzu shima bai ce komai ba.