By Abbas Yakubu Yaura
Wani matashi daya kammala karatun NCE mai suna Idris Shuaib mai shekaru 22 ya kashe kansa a jihar Kwara.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a garin Gwanara dake karamar hukumar Baruten ta jihar.
Marigayi Idris ya fito ne daga harabar Wooro na Ankara, kuma ‘yan uwa sun gano gawarsa a rataye a jikin bishiyar kashu.
Rahotanni sun bayyana cewa ya rataye kansa ne saboda rashin iya yin jima’i, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.Ba a fayyace ko batun ya faru ne saboda rashin lafiya ko kuma matsalar zamantakewa ba.
Sai dai wakilinmu ya samu labarin cewa marigayin ya yi yunkurin kawo karshen rayuwarsa a baya saboda matsalar.
Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa marigayin ya rataye kansa ne a cikin gonar mahaifinsa dake kan titin Gwanara- Munduro tare da taimakon igiya da jarka. .
Mahaifinsa, Malam Muhammad Idris, ya bayyana shi a matsayin wanda ya kammala karatunsa a Kwalejin Ilimi ta Muyideen, Ilorin (Gwanara Campus).
Afolabi ya kara da cewa, “Amma an sauko da gawarsa daga bishiyar kuma an kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa yayin da ake ci gaba da bincike”.