Wani dan kasar China ya daba wa masoyiyarsa wuka, wata matashiya ‘yar shekara 23 a duniya a Janbulo, karamar hukumar Kumbotso a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’ar nan bayan wanda ake zargin ya kawo wa marigayiyar ziyara, mai suna Ummakulsum Sani Buhari, a gidan iyayenta da ke kusa da ofishin hukumar kula da muhalli ta Kasa (NESREA).
Yayin da abin da ya faru a tsakanin masoyan da ya kai ga faruwar lamarin ya kasance cikin zance, Daily trust ta tattaro cewa likita ne ya tabbatar da mutuwar ta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wani makwabcin marigayiyar Abubakar Mustapha ya shaida wa Daily trust cewa ita matar ta taba yin aure kuma wadda ake zargin saurayinta ne.
Karanta kuma: Wata Kotu Ta Daure Wani Dan Kasar China A Gidan Yari
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren jiya. Wanda ya kashe ta saurayinta ne tun kafin ta yi aure. Mijinta ya sake ta suka ci gaba da zumunci a matsayin saurayi da budurwa. Ya dinga zuwa gidanta. An kai ta asibitin UMC Zhair wanda bai fi kilomita daya da gidanta ba kuma ta rasu.”
“Khaleed yayanta ne ya hana ’yan unguwar da suka afkawa wanda ya yi kisan a lokacin da ya tafi motarsa lokacin da ya shiga gidan, saboda a tunaninsa (Khaleed) zai yi wani abu na daban. Daga nan aka kama mutumin, aka mika shi ga ‘yan sanda,” in ji Mustapha.
Wani makwabci mai suna Muhammad Sani ya shaida wa daya daga cikin ‘yan jaridarmu cewa wanda ake zargin ya taba yunkurin kashe kansa saboda budurwar amma da ‘yan sanda suka shiga tsakani aka daidaita lamarin.
“Lokacin da za ta yi aure, ya taba yunkurin kashe kansa saboda kaunar da yake mata har sai da ‘yan sanda suka shiga tsakani kuma komai ya daidaita,” in ji shi.
Ya kara da cewa an kai wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Dorayi.
Marigayiyar, Ummakulsum wadda aka fi sani da ‘Ummita’ ta yi makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin bayar da karin bayani daga baya.
A wani labarin kuma: Wani Mutum Guda Ya Rasa Ransa A Wani Gini Da Ya Rushe
Akalla mutum guda ne ya rasu a wani gini da ya ruguzo da sanyin safiyar ranar Asabar a karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:47 na asubahin wannan ranar ta Asabar.
TOU ALLAH YAGAFARTAMATA