By Abbas Yakubu Yaura
Ana zargi wani matashi mai matsakaicin shekaru mai suna Oyakemeagbegha da kashe wani mutum mai suna Mista Ebitein Aperebo, a unguwar Ojobo, a karamar hukumar Burutu ta jihar Delta.
Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar bayan wanda ake zargin ya samu sabani da matar wanda abin ya shafa.
A cewar majiyoyi, Oyakemeagbegha, bayan rashin jituwar, ya ci gaba da ganawa da mijin matar a gida domin kara huce haushinsa.
An tattaro cewa wanda abin ya shafa yana barci lokacin da Oyakemeagbegha ya afkawa gidan, inda ya tashe shi daga barci “ya buge shi da itace 2/2 tare da kashe shi har lahira.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Oyakemeagbegha ya gudu ne bayan ya aikata laifin dan gujewa binciken jami’an tsaron ‘yan sanda.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, an kasa samun jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.