Wani Mutum Dan kasar Congo Mai suna Luwizo ya yi namijin kokari wajan auran mata uku wadanda dukkanninsu suka fito daga tsatso guda.
Mai shekaru 32 ya bayyana cewa ya hadu da daya daga cikin amarannasa ne Mai suna Natalie a kafar sada zumunta na Facebook, inda suka fara tattaunawa Kuma soyayya ta shiga tsakanin su, Wanda daga bisani Kuma shuka yanke shawarar haduwa da juna, kamar yadda Jaridar Afrimax English ta ruwaito.
Ya Kuma bayyana cewa Natalie ta Gabatar da shi ga sauran Yan uwanta mata Nadege da kuma Natasha, wadanda daga bisani suma suka tsunduma da kaunarsa.
Wizo Wanda sunansa na gayu kenan ya ce, ya matukar razana a lokacin da ya hadu da Matan na shi Yan uku, yayin da ya ziyarci gidan su Natalie domin neman auren su dukka.
“Nayi matukar razana, domin har na kusan suma, na daukama mafarki nakeyi ” inji shi
Kazalika ya bayyana cewa, tun da Yan ukun sun shaku da juna Kuma bazai yiwu a raba su ba, sun zabi su auri Miji guda.
Da aka tambaye su yadda suka gudanar da lamarin, daya daga cikin ‘yan ukun ta ce, “Da muka ce masa dole ne ya aure mu mu duka, sai ya yi mamaki. Amma da yake yana kaunarmu duka, babu abin da ya hana mu shirin auren, tun da mu ma muna ƙaunarsa.
A karshe a nashi bangaren Luwizo ya ce duk da cewa iyayensa ba su amince da hukuncin da ya yanke ba, kuma sun yanke shawarar kin sanyawa auren nasa albarka, amma bai yi nadama ba game da lamarin.