By Abbas Yakubu Yaura
Wani mutum mai suna Mohammad Bagudu Abdulrahman Lapai da matarsa Khadijat mai juna biyu sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Suleja ta jihar Neja.
Dan ma’auratan mai shekaru 3, ya tsira daga hadarin da ya faru da sanyin safiyar Lahadi, 13 ga watan Fabrairu.
A cewar wani Kwamared Lanre Sadiq, yaron a halin yanzu yana samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Wani ban gare na rubutun yana karantawa: “ME ALLAH BA ZAI IYA YI ba? Amir dan marigayi Mista Mohammed Bagudu Abdulrahman wanda ya rasu a safiyar yau a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Suleja daga karshe ya tsira.
“Da farko an ba da rahoton cewa ya mutu amma labari mai dadi shine, Amir ya tsira yayin da iyayen suka yi hatsarin a safiyar yau.
“Yaron mai shekaru 3 mai al’ajabi yana samun kulawa a halin yanzu. Mu yi wa wannan yaron da ba shi da laifi addu’a ya tsira daga wannan bala’i. Uban, Malam Abdulrahman Bagudu da matar mai ciki duk sun mutu.
“Hakika Allah madaukakin sarki mai girma ne, Allah ubangiji ya jikan iyayensa da rahama ya kuma baiwa iyalansa kwarin gwiwa wajen karban nufin Allah madaukakin sarki, ya kuma kiyaye karamin yaro ya kuma bashi lafiya.”