Daga: Abbas Yakubu Yaura
Mamallakin kamfanin ‘Always Petroleum and Energy Service Limited’ Alhaji Mohammed Jamiu ya samu ‘yanci, bayan shafe sama da watanni biyu a hannun wadanda suka sace shi.
Daily Trust ta rawaito cewa an yi garkuwa da Jamiu ne a ranar 9 ga watan Yuli, 2022 a gidansa da ke Idare a karamar hukumar Okene a jihar Kogi yayin bikin Sallah.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shida Daga Cikin Hamshakan Attajiran Yara A Najeriya
An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun kai kimanin hudu sun shiga gidansa ne jim kadan bayan ya dawo daga filin sallar idi, inda suka yi kamar ‘yan kasuwa.
Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an sako dan kasuwar ne a daren ranar Alhamis.
Majiyar ta kara da cewa iyalan sun biya kudin fansa mai ma’ana kafin wadanda suka sace shi su sako shi.
“Sun saki dan uwanmu, Alhaji Mohammed Jamiu Idris. Sama da wata biyu kenan muna addu’a domin ganin hakan ya tabbata. Duk da cewa mun biya kudin fansa domin a sake shi, muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya dawo da rai,” inji majiyar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da hamshakin dan kasuwar man ya yi arangama da masu garkuwa da mutane ba.
An bayyana cewa an sace Jamiu ne a shekarar 2019 a daya daga cikin gidajen mai da ke Okene, amma jami’an soji suka ceto shi bayan wasu kwanaki da aka yi garkuwa da shi.
A yayin aikin ceton, an yi zargin cewa sojoji sun yi asarar jami’insu, yayin da daya daga cikin masu garkuwar kuma ya mutu.
A wani labarin kuma, Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Miliyan 304 A Matsayin Alawus Ga Jam’iar YMSU
Gwamnatin jihar Kano ta amince da biyan Naira miliyan 304 a matsayin alawus-alawus ga ma’aikatan jami’ar Yusuf Maitama Sule (YMSU), daya daga cikin jami’o’inta.
Wannan amincewar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta yi kira ga ma’aikatan ilimi da su koma azuzuwa su fice daga yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi.