By Abbas Yakubu Yaura
Wani direban babbar mota mai suna Moshood Gbadamosi ya kashe ‘yan uwa biyu, Olamide Opayemi mai shekaru 14 da Damilola Opayemi mai shekaru 11 a yankin Ilisan-Remo da ke jihar Ogun a ranar Juma’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa lamarin ya faru ne daura da shagon gyaran gashi na mahaifiyarsu.
Wani makwabci su mai suna Olayinka Oremuyiwa wanda ya zanta da wakilinmu, ya ce Gbadamosi ya bugi yara hudu ne a lokacin da suke tsaye a bakin hanya.
“Biyu daga cikinsu sun tsira, amma Olamide,na biyu wanda zai cika shekaru 15 a watan Maris, da Damilola, wanda aka haifa na karshe, sun mutu,” in ji ta.
Oremuyiwa ya bayyana cewa an garzaya da yaran zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Babcock, inda aka tabbatar da mutuwarsu.
Ta ce, “Lokacin da na isa wurin, na ga mutane da yawa sun taru. Na ga mahaifiyarsu, Abosede, tare da Olamide. Mun yi ƙoƙarin tsayar da wasu motoci don kai yarinyar asibiti, amma babu wanda ya tsaya. Na ga wani dan banga na ce ko zai iya taimaka mana mu dauke ta, amma ya ki. Dole ne in tallafa wa mahaifiyar kuma muka kai yarinyar asibiti a kan babur.
“A can ne na samu labarin cewa Damilola, karamar yarinya an kaita asibiti tun da farko.”
Wani shaidan gani da ido, Shola Emmanuel, ya ce ‘mun dauki matakin ne biyo bayan lamarin kafin ‘yan sanda su shiga tsakani.
Ya ce, “Kowa ya fusata domin wannan ba shi ne karon farko da faruwar hakan a Ilisan ba. Wadannan samarin kawai suna tuki cikin sakaci; ba su damu da komai ba. Mutane sun kusa kona motar.”
Wani kawun mamacin, Yomi Opayemi, wanda ya yi magana da iyalan, ya ce an gurfanar da wanda ake zargin a kotu.
Ya kuma ce an dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Janairu domin cigaba da sauraren karar.
Yomi ya ce, “Moshood Gbadamosi ya bayyana a gaban wata kotun majistare da ke Ikenne Remo ranar Litinin. Alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari. A bar shi ya fuskanci adalci; abin da muke bukata ke nan. Barazana ba za ta hana kukanmu na neman adalci ba.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya yi alkawarin komawa ga wakilinmu kan lamarin. Har yanzu dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.