By Abbas Yakubu Yaura
Wani direban mota da har yanzu ba a tantance ba ya bace bayan daya murkushe wani mahayin babur daya aike shi har lahira a kusa da wurin tsayawar motoci dake Charly, a babban titin Gbagada a jihar Legas.
Sai dai kuma wani mahayin mai suna Emmanuel Odoh, ya tsallake rijiya da baya a lokacin da direban ya kara tunkudashi gaba tare da mamacin.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa wadanda lamarin ya rutsa dasu suna kan hanyarsu ta zuwa wata hanya a jihar ne a ranar Larabar data gabata, sai direban daya yi batan dabo, wanda ke tsaka da gudun wuce sa’a, ya afka masu.
Odoh ya ce da sanin abin da ya aikata, direban ya gudu daga inda lamarin ya faru, inda ya kara da cewa wasu fusatattun mutane sun banka ma motar sa wuta.
Ya ce, “Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na ranar Laraba.Ina aiki da kanti akan layi, Jumia. Na ɗauki oda na je in kai shi a Mende, Maryland. Ina kan hanyata ta dawowa, sai na ga direban motar Hilux ya nufi hanyar da nake yi da gudu.
“Na yi sauri na nufi gefen titi ina cikin haka sai na ci karo da wani mahayin ya she a gabana. Amma yayin da na kalli madubi na don sanin abin da ke faruwa a bayana, sai naga mai Hilux ya murkushe su duka.
“Na yi nasarar tsallakewa kan motar Toyota Camry. Da direban ya gan ni, sai ya rage gudu, a haka ne na yi nasarar tserewa. Amma dayan mai jigilar kaya bai yi sa’a ba; tasirin karo ya jefa shi sama. Inda hular kwanon dake kansan ta cire goshinsa ya bugu a kasa. Ya rasu jim kadan bayan haka.
“Matukin motan da wanda ke tare da shi da sauri suka sauka suka yi kamar suna neman agaji, amma suka gudu.
Da mutane sun kama su, amma suna tunanin dayan bai mutu ba. Don haka, saboda bacin rai, yaran yankin sun kona motar.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, ya ce zai koma ga wakilinmu bayan an yi masa karin bayani.
Har yanzu bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto.