By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wani mummunan hatsarin mota ya afku a mahadar Obinaetiti Akwuzu ta hanyar Nteje-Onitsha, da yammacin ranar Juma’a a jihar Anambra.
A cewar wani ganau, hatsarin ya faru ne tsakanin motoci biyu: direban wata shudiyar Mercedes 911 mai lamba XA129AWK da ba’a tantance ko wanene ba a cikinta, sai kuma direban motar Honda Accord mai lamba RBX155PC da shima ba’a tantance ko wanene ba.
Mai yiwuwa musabbabin hatsarin na da nasaba da cikas da kuma wuce gona da iri yayin tuki.
Wani shaidan gani da ido ya ce hatsarin ya afku ne lokacin da direban motar kirar Honda da ke tukin motar cikin tsananin gudu ya bugi mota kirar Mercedes Benz 911 daga baya.
Direban motar kirar Mercedes Benz 911 ya hango tulin yashi da tsakuwa a kan titin sai ya yi saurin kaucewa hanya yayin da direban motar kirar Honda da bai lura ba, ya kutsa cikin motar ya yi karo da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa wani kamfanin gine-gine ne ke amfani da yashin.
Wasu manya mutane maza uku ne hatsarin ya rutsa dasu, An ceto mutane biyu ba tare da jikkata ba yayin da mutum daya ya mutu
Ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, an ajiye mamacin a dakin ajiye gawa na Wisdom, Awkuzu.
Jaridar Dimokuradiyya Motar dai an kai ta ofishin hukumar kiyaye hadurra ta tarayya dake Nteje, yayin da ake kokarin ganin an kawar da cikas din kanhaya da jami’an ceto suka yi.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Anambra, Adeoye Irelewuyi, ya jajantawa iyalan mamacin.
Ya kuma gargadi jama’a masu tuka mota da su guji wuce gona da iri yayin gudanar da tuki da kuma kasancewa cikin shiri yayin tuki.
Ya kara da cewa “Dole ne a bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kowane lokaci dan kaucewa afkuwar hatsari.”