Kungiyar kiristoci ta ‘The Pentecostal Bishops Forum’ na jihohin arewa 19 a Nijeriya (PBFNS), sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sanya jami’an tsaro a kafatanin al’ummar Kudancin jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar ta PBFNS, John Praise Daniel, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, inda ya ce ya zama wajibi a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Kudancin jihar Kaduna.
Bishop Daniel wanda shi ne ya assasa Cocin ‘Dominion Chapel International Church’, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta cafke tare da hukunta wadanda suke da hannu da kuma masu daukar nauyin kashe-kashen da ake yi a duk inda suke.
A cewarsa, ya kamata gwamnati kuma ta biya diyyar wadanda aka lalatawa dukiya, tare da wadanda suka rasa ‘yan’uwansu da wadanda aka raunata. Sannan har wala yau ya yi kira da a samu hadin kan Sarakuna da Malaman addini domin tattaunawa da sauran kungiyoyi daban-daban domin samun mafita.