Wani Fasto mai shekaru 54 a duniya, ya shiga hannun hukumar ‘yan sanda bayan zargin sa da ake na yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade a jihar Ogun.
Mahaifin yarinyar ya yi ƙarar Faston, mazaunin Itele Ota a jihar Ogun ne bayan maƙwabta sun sanar da shi cewa ya lalata masa yarinya.
https://dimokuradiyya.com.ng/fyade-yan-sanda-sun-kama-wanda-ya-yi-wa-mai-ciki-fyade-a-jihar-oyo/
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Jaridar Daily trust cewa, “Wanda ake zargin, wanda ya ce shi Fasto ne, ya ce ya lalata yarinyar ne a cikin wani kango bayan ya yauɗare ta a lokacin da ya gan ta tana yawo”.
Abimbola ya ce mutumin da ya ce shi Fastoasto ne a cocin Helmet Life, “Ya rabu da matarsa tun a shekarar 2016”, kuma bayan bincike za a gurfanar da shi a kotu.