A ƙalla mutane biyi sun gamu da ajalinsu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon ruftawar wani ginin bauta ta Yahudawa a birnin Kudus.
Hukumomin Yan sanda sun ce a kalla yahudawa masu bauta sama da 600 ne ke bauta yayin da ginin ya rufta a kusa da West Bank.
Jama’a da dama sun ga ta kansu yayin ibtila’in inda suke faduwar kifin gwangwani, wani a kan wani.
Wannan jarabawa ta faru ne yan makonni bayan mutane sama da arba’in suka rasa rayukansu yayin wani turmutsitsi da ya auku a gurin wani shagalin bikin yahudawa na shekara-shekara a kasar.
Da ma dai an bayyana cewa ginin tun a farkonsa yana da rauni gurin tsarinsa da kuma diri.