Daga Abdullahi Kebbi
Wani gini da ake tsakiyar ginawa mai Hawa uku ya rufta a jahar delta.
Ankuma tabbatarda rasuwar mutane hudu a Garin abraka dake karamar hukumar Ethiope ta gabas dake jahar ta delta.
Babu tabbas akan rukitowar ginin, to amma ginin ya rikitone a lokacinda ake tsakiyar tafka ruwan sama a Garin.
Haka an bayyana cewa ginin ya rufta kan wasu leburori da suka labe a cikin ginin a lokacinda suke ginin, suna zaman jiran a dauke ruwan sai suci gaba da gini sai akayi rashin sa’a ginin ya ruftamusu.
A tsakanin yan makwannin nan ansha samun irin wadannan matsaloli na ruftawar gine-gine musamman a kudancin najeriya.