Wani ginin bene da ya rufta a unguwar Gwammaja ’yan Ƙosai da ke ƙaramar hukumar Dala a ƙwaryar birnin Kano, ya hallaka mutane biyu yayin da mutane takwas suka jikkata.
Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jihar Kano, Sa’ idu Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin da cewa jami’an hukumar sun ceto mutum takwas da ransu waɗanda ginin benen ya danne, sun kuma gano gawawwakin mutane biyu daga baya.
Muhamamd ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, domin basu agajin gaggawa.
https://dimokuradiyya.com.ng/wani-gini-ya-rufta-a-jihar-delta/
“Da misalin ƙarfe 1:37 na ranar Talata 15 ga watan Satumba muka samu labarin rushewar benan kuma nan take jami’anmu suka isa wurin domin kai ɗauki.”
“Ginin benen mai hawa ɗaya ya danne mutane 10 da ke cikin gidan inda muka ceto takwas daga cikin su yayin da likitoci suka tabbatar da Allah ya yiwa mutane biyu cikawa”, inji shi.
Sa’idu Muhammad ya yi kira ga jama’a a jihar da su dinga lura da yanayin mahallin da suke zaune domin kare aukuwar irin haka.