Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jami’an ‘yan sanda daga sashin Iheagwa na jihar Imo, sun cafke wani gujajjen Fursuna mai suna Justice Anokam, bisa zarginsa da daba wa wata mata mai juna biyu wuka inda ya hallakata da ita da jarinnata a unguwar Umuejechi Nekede mai cin gashin kanta da ke karamar hukumar Owerri ta Yamma.
Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa wanda iftila’in ya afkawa, tana zune a gidan haya a yankin amma yar asalin karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo ce.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Shiga Rudani Da Rikici Kan Zargin Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi ‘Yan Sa’oi Da Sallamar Mataimakin Sa
Wani mazaunin garin Iyke Opara ya ce matar mai ciki ta fito ne daga babbar mahadar Ama-Ato kafin wanda ake zargin ya farmake ta.
Opara ya ce wanda ake zargin yana addabar al’umma tun bayan da ya tsere daga gidan yari a watan Afrilun shekarar 2021 a Imo.
Wanda ake zargin, wanda ya yi ikirarin cewa yana shan kwaya ne lokacin da aka tambaye shi a cikin wani faifan bidiyo da ke tada hankali, an ce ya fusata kuma ya gangaro kan matar lokacin da ya ke dauke da wukar bayan ya bukaci ta ba shi kudi ya ci abinci sai ita kuma ta guje shi.
A cewar majiyar, ta ce masa ya kula da harkokinsa kuma hakan ya fusata shi. Ya cire wata wuka da ya boye a cikin wando, ya daba mata a ciki.
Majiyar ta ce matar ta yi asarar jini mai yawa kuma ta rasu ne a lokacin da aka garzaya da ita zuwa asibiti.
Ya ci gaba da cewa wanda ake zargin ya gudu nan take amma matasan yankin sun bi sawu suka kama shi bayan sun yi yunkurin daba masa wuka shima.
Anokam mai shekaru 30 da haihuwa, tun da farko ‘yan bangar Nekede ne suka kama shi kafin su mika shi ga jami’an ‘yan sanda na sashen ‘yan sanda na Ihiagwa a daidai lokacin da matasan yankin suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin hallaka shi kafin ‘yan sanda su shiga tsakani.
Kakakin ‘yan sandan, Micheal Abattam, lokacin da aka tuntube shi ya ce yana jiran rahoton halin da ake ciki daga sashin.