Kociyan Arsenal Mikel Arteta ba ya cikin hadarin rasa aikinsa, duk da yadda kungiyar ta fara gasar Premier da rashin sa’a. An rika yada cewa tsohon kociyan Chelsea Antonio Conte ne zai maye gurbinsa. (Independent)
Paris St-Germain na son Real Madrid ta lale mata yuro miliyan 220 (fam miliyan 188) idan har tana son dan gabanta na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22. (Jaridar Le Parisien)
Manchester City ba ta kawar da yuwuwar sayen dan gaban Juventus da Portugal ba Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, bayan da kyaftin din Ingila Harry Kane ya tabbatar da ci gaba da zamansa a Tottenham. (Jaridar ESPN)
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalejin Ilimi ta Zamfara ta tabbatar da Barazanar Yan bindiga
Kane ya damu ganin yadda shugaban Tottenham Daniel Levy bai zai yarda a sayar da shi ba, wanda hakan ya sa dan wasan mai shekara 28, zai kulla sabuwar yarjejeniya wadda za ta kunshi damar barinsa ya tafi. (Telegraph)
Pep Guardiola zai bar Manchester City idan kwantiraginsa ya kare bayan kakar 2022-23, sannan ya dauki hutu daga harkar kwallon kafa, kafin daga bisani ya karbi aikin horad da tawagar kasa. (Globo, daga Manchester Evening News)
Kociyan Roma Jose Mourinho na shirin taya dan wasan tsakiya na Chelsea, dan Ingila Ruben Loftus-Cheek fam miliyan 13 da rabi. Dan wasan mai shekara 25 ya yi aiki na dan lokaci da Mourinho a karo na biyu da kociyan ya horad da Blues. (Mail)
Manchester United ba za ta iya taya ko dai dan wasan tsakiya na Rennes, dan Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 18, ba ko kuma dan wasan tsakiya na Atletico Madrid dan Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26 ba, sai dai idan za ta sayar da wasu ‘yan wasanta ta samu kudin cinikin. (ESPN)
Comments 1